An tambayi Uwar Muminai A'isha Allah Ya yarda da ita, a kan ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ta amsa, da jawabi gamamme, ta kuma mayar da mai tambayar zuwa Alƙur’ani mai girma wanda ya ƙunshi dukkanin siffofi na kamala, sai ta ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ɗabia’antuwa ne da ɗabi’u na Alƙur’ani, abin da Alƙur’ani ya yi umarni ya yi, kuma abin da Alƙur’ani ya hana ya nisance shi, sai ɗabi’unsa suka kasance aiki da shi da tsayawa inda ya iyakance, da ladabtuwa da ladubansa da ɗaukar izina da misalai da ƙissoshinsa.