Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya yi addu'a sai ya ce: Ya Allah ? Kaɗai ni mutum ne, ina yin fushi kamar yadda ɗan Adam yake yin fushi, duk muminin da na cutar da shi ko na zage shi na aibanta shi, ko na tsine masa na yi masa mummunar addu'a da korewa daga rahamarKa, ko na dake shi da bulala, to ka sanya hakan ya zama tsarkaka da kusanci da tsarkakewa da kaffara da kuma rahamar da zaka yi masa rahama da ita.