An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da shugabannin da suke neman haƙƙinsu daga mutane na ji da biyayya, kuma suna hana haƙƙin da ke kansu; na yin adalci da bada ganima da dawo da abubuwan da aka zalinta da daidaito, to me zaka umarcemu mu aikata tare da su? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kau da kai; kamar ya ƙyamaci waɗannan tambayoyin, sai dai mai tambayar ya sake maimaita masa karo na biyu da na uku, sai al-Ash'as ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya fizgo mai tambayar dan ya sa shi ya yi shiru. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa, ya ce: Ku ji abinda suke faɗa, kuma Ku bi umarninsu; kaɗai abinda aka ɗora musu na adalci da bawa talakawa hakkinsu yana kansu, kuma abinda aka ɗora muku na biyayya da bada haƙƙoƙi da haƙuri akan masifu yana kanku.