Sahabi mai girma Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin: Cewa sun fita a dare mai yawan ruwa, kuma duhu ya kasance mai tsanani dan neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; Domin ya yi musu sallah, sai suka same shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: "Ka ce" wato ka karanta, bai karanta komai ba, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sake fada masa, sai Abdullahi ya ce: Mezan karanta ya Manzon Allah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka karanta Surat Al-Ikhlas {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai}, da Falaki da Nasi {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina nemn tsari da Ubangijin mutane}, a lokacin yammaci, da lokacin safiya, sau uku za su kiyayeka daga kowanne sharri, kuma zasu kareka daga kowanne mummunan abu.