Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce da safiyar kowace rana bayan ɓullowar alfijir, da yammacin kowane dare kafin faɗuwar rana sau uku: (Da sunan Allah) ina neman taimako ina neman kiyayewa daga dukkan abinda yake cutarwa (wanda ba ya cutarwa tare da) ambatan (sunanSa), ko (wane abu) duk irin girman da ya yi (a cikin ƙasa) da abinda yake fitowa daga gareta na bala'i (ko a cikin sama) mai saukowa daga gareta na bala'i (Shi Mai yawan ji ne) ga maganganun mu (Masani) da halayenmu. Wanda ya faɗeta lokacin da ya shiga maraice bala'i ba zai same shi ba bagtatan har sai ya wayi gari, wanda kuma ya faɗeta lokacin da ya wayi gari bala'i bagtatan ba zai sameshi ba har sai ya shiga maraice. Sai maruwaicin hadisin Aban ɗan Usman ya samu cutar shanyewar ɓarin jiki; shi ne shanyewar ɓarin jiki, sai mutumin da ya ji hadisin a wunsa ya fara kallon Aban yana mai mamaki! sai mutumin ya ce: Me ya sameka ne kake kallona?! Na rantse da Allah ban yi wa Usman ƙarya ba, kuma Usman bai yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya ba, saidai a ranar da abin ya sameni a cikinta Allah bai ƙaddara mini faɗinta ba, fushi ne ya sameni sai na manta in faɗi waɗannan kalmomin da aka ambata.