explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum yana ci da hannunsa na hagu, sai ya umarce shi da ya ci da hannunsa na dama, sai mutumin ya amsa masa dan girman kai da karya da cewa shi ba zai iya ba! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mummunan addu'a akansa da haramta masa ci da dama, sai Allah Ya amsa addu'arsa da shanyewar hannunsa na dama, bai kara daga shi zuwa bakinsa ba bayan hakan da abinci ko abin sha.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • wajabcin ci da dama, da haramcin ci da hagu.
  • Girman kai daga aikata hukunce-hukuncen shari'a mai aikata shi yana cancantar ukuba.
  • Girmamawar Allah ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da amsa addu'arsa.
  • Halaccin umarni da aikin alheri da hani daga abin ki a kowanne hali har a cikin halin ci.