Daga Abu Hurairah, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai taba zagin abinci ba, idan ya so shi, ya ci, in kuma ya ki shi, to ya bar shi. Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi