Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji wani sauti (kara) mai tsoratarwa kamar faɗuwar wani jiki daga jikkuna, sai ya tambayi waɗanda ke tare da shi cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - game da wannan karar, sai suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai wanann karar da kuka ji ta ta wani dutse ce da aka yi jifa da shi daga gefen Jahannama tun shekara saba'in, shi yana sauka yana faɗawa a cikinta, har sai ya kai karshenta a yanzu lokacin da kuka ji sautin.