Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da umarnin sauƙaƙawa da rangwame wa mutane, da kada a tsananta musu a dukkanin lamura na addini da na rayuwa, wannan kuwa a daidai yadda Allah Ya halatta Ya kuma shar’anta. Kuma yana kwaɗaitarwa a kan bushara da alheri, da rashin korar (kyarar) mutane.