explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda baya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba, to, jin ƙan bawa ga halitta yana daga mafi girman sabubban da ake samun rahamar Allah da su.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Jin ƙai abin nema ne ga sauran ababen halitta, sai dai an keɓanci mutane da ambato ne don ba da muhimmanci garesu.
  • Allah Shi ne Mai jin ƙai, kuma Yana jin ƙan bayinsa masu jin ƙai, to, sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki.
  • Jin ƙai ga mutane ya tattaro alheri garesu da tunkuɗe sharri garesu da mu'amalantarsu da kykkyawa.