Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikin wasu mutane cikin sahabbansa suna zaune sai ya tambayesu, shin bana sanar daku in tunatar muku wanda yake shine mafi alherinku da wanda yake shine mafi sharrinku ba? Da ba su yi magana ba kuma basu amsa masa da komai ba, dan jin tsoron banbance alherinsu da sharrinsu, suka ji tsoron kunyata sai suka yi shiru. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sake yi musu tambaya sau uku, sai wani mutum daga cikinsu ya amsa: Eh ya Manzon Allah, bamu labarin mafi alherinmu daga mafi sharrinmu. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana musu: Cewa mafi alherinku shine wanda ake sauraro kuma ake fatan (samun) alherinsa da kyautatawarsa da alherinsa, kuma ake amincewa sharrinsa dan haka ba'a jin tsoron ta'addancinsa da munanawarsa da kuma zalincinsa, kuma mafi sharrinku shine wanda ba'a fata kuma ba'a sauraro ba'a kwaɗayin alherinsa da kyautatawarsa da alherinsa, kuma ba'a amincewa sharrinsa, kai ana jin tsoron ta'addancinsa da munanawarsa da kuma zalincinsa.