Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - a sashin hanyoyin Madina, Abu Huraira ya kasance yana da janaba, kuma yana daga cikin girmamawarsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ƙyamaci zama da shi da kuma hira da shi alhali shi yana kan wannan halin dan yana zatan cewa shi najasa ne, sai ya tafi a ɓoye ya yi wanka, sannan ya dawo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye shi ina ya tafi? Sai ya sanar da shi halin da yake ciki, kuma cewa shi ya ƙyamaci zama da shi ne alhali shi yana najasa saboda janabar (da ta same shi), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mamaki kuma ya ce masa: Lallai cewa mumini mai tsarki ne ba ya zama najasa akan kowane hali; a raye ko a mace.