Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mai sallah idan ya yi taraddudi a cikin sallarsa bai san nawa ya sallata ba, shin uku ne ko huɗu? to ya nisantar da adadin da ya yi kokwanto cikinsa kada ya yi anfani da shi; ukun su ne abin da aka yi yaƙini akan su, sai ya sallaci raka'a ta huɗu, sannan sai ya yi sujjada kafin ya yi sallama. Idan abinda ya sallata huɗu ne a haƙiƙa; to sun zama biyar in an kara raka'ar, sajadodi biyun na rafkanuwa canji ne ga raka'a, sai adadin ya zama biyu kenan ba ɗaya ba, idan kuma ya sallaci huɗu ne da wannan raka'ar ta ƙari; sai ya zama ya bada abinda ke kansa ba tare da ƙari ko ragi ba. Sujjada biyun na rafkanuwa sun zama ƙasƙantarwa ga Shaiɗan da kuma halakarwa gare shi, da dawo da shi a taɓe abin nisantarwa daga manufarsa; domin shi ya cakuɗa masa sallarsa, ya bijiro dan ɓata ta, kuma sallar ɗan Adam ta cika yayin da ya yi riko da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki - da yin sujjadar da Iblis ya saɓa maSa da ita, lokacin da ya ki biyayya ga Allah da yin sujjada ga (Annabi) Adam.