Maazanni sune mafi cikar hankalin Mutane, kuma sune mafi tabbatar zukata, kuma sune mafi tsayuwa da hakkin Allah, amma duk da hakan basu futa daga iyakar Mutane ba, Mazon allah shi ne mafi cikar sifofi, kuma duk da haka wani lokaci Mantuwa takan bujuro masa, sabida kasancewa dan adam ne, kuma Abu huraira ya rawaito cewa Annabi yayi sallah da sahabbansa kodai Sallar azahar ko kuma La'asar kuma cewa Abu Huraira ya fade ta amma kuma Dan Sereen ya manta ta, yayin da yayi Sallah Raka'a biyu na farko sai ya yi Sallama, kuma yayin da ya kasance Annabi Mutum ne cikakke, ransa ba zai nutsu ba sai da cikakken aiki, sai yaji a jikinsa cewa akwai tawaya da kuma wani abu bai cika ba, kuma baisan mai ya jawo shi ba, sai ya tashi zuwa wani ita cce da aka ajiye a gaban alkiblar Masallacin kuma ya kashingida a kansa ransa yana sosuwa, kuma ya hade yan yatsunsa, kuma masu saurin futa daga Masallaci suka futa suna ganawa a tsakaninsu, cewa wani abu ya faru fa, shi ne an rage Sallah, kamar sunji nauyin Annabi ne cewa yaya zai yi kamarsa yayi mantuwa, kuma sabida kwarjininsa a zukatansu babu wanda ya iya bugar kirji da ya tambaye shi akan wannan Mai muhimmanci, cikin wadanda suke wurin har da Abubakar da Umar -Allah ya yarda da su, Musamman daman sun lura da damuwarsa da kuma kebancewarsa, sai dai wani Mutum daga cikin Sahabbai ana kiran Zulyadainshi ya yanke wannan shiru din, ta hanayar tambayarsa Annabi da cewa: Ya Manzon Allah wai Mantawa kayi ne? domin babu wanda ya iya tambaya kowanne ya yanke cewa wannan hakan zai iya faruwa, sai Annabi ya ce: yana mai gini zatonsa, ba'a rage ba kuma ba mantawa nayi ba, sai Annabi yai nufin ya tabbatar da ingancin abinda zulyadaini yake fada, domin ya sabawa zaton sa na cewa Sallar ta cika ko bata cika ba ne abinda zai rinjayar da fadinsa, sai ya ce ga wadanda suke gefensa na Sahabbansa: Haka yake abinda Zulyadain yake fada raka'a biyu kawai nayi? sai suka ce: Ey a lokacin sannan Annabi ya shige gaba ya kawo abinda ya bari na ragowar sallar, kuma bayan yayi tahiya sai yayi sallama sannan yayi Kabbara kuma yana zaune, kuma yayi Sujada kwatankwacin sujadar ainahin Sallah ko mafi tsawo daga ita, sannan ya dago kansa sannan yayi kabbara, sannan ya kuma yin kabbara kuma yayi sujada kwatankwacin sujada ko mafi tsawonta, sannan ya kuma dago kansa kuma yayi kabbara, sannan yayi sallama kuma bai tahiya ba.