Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayiwa Sahabbansa Sallar Azahar,yayinda ya sallaci raka'oi biyun farko,sai ya tashi a bayansu,bai yi zaman Tahiya na farko ba,sai Mamu suka bishi a bisa hakan.Har sai da ya sallaci raka'o'i biyun karshe,kuma ya zauna don Tahiyar karshe,ya gama ta,Mutane suka jirayi sallamarsa,sai yai kabbara alhali yana cikin zamansa,sai yayi sajada dasu sajadu biyu kafin yayi sallama kwatankwacin sajadar cikin Salla,sannan yayi sallama.wannan sajadar ta kasance gyara ga Tahiyar da ya bari.