Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da falalar gaggawar tafiya zuwa sallar Juma'a. Gaggawa tana farawa ne daga bullowar rana zuwa lokacin zuwan liman; shi ne sa'o'i biyar, ana karkasasu kaso biyar gwargwadan lokaci tsakanin bullowar rana har zuwa shigowar liman da hawansa minbari dan huɗuba: Na farko: Wanda ya yi wanka cikakke kamar wankan janaba, sannan ya tafi masallacin Juma'a a lokaci na farko kamar ya yi sadaka da taguwa ne. Na biyu: Wanda ya tafi a lokaci na biyu kamar ya yi sadaka da saniya ne. Na uku; Wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya yi sadaka ne da rago - shi ne namijin tinkiya - mai ƙahuhhuna. Na huɗu: Wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya yi sadaka ne da kaza. Na biyar: Wanda ya tafi a lokaci na biyar kamar ya yi sadaka ne da ƙwai. Idan liman ya fito dan huɗuba; sai mala'ikun da suke zaune a ƙofofi dan rubuta masu shiga masallaci na farko da mai biye da shi sai su dakatar da rubutu, sai su zo suna jin zikiri da huɗuba.