explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ya zo na Ramadan yana ƙoƙari a cikinsu da yin ibada da ɗa'a, kuma yana kai matuƙa a cikin nau'ikan alherai da sinfofin ayyukan kirki da ibadu mafi yawa daga abinda yake ƙoƙari a cikin waninsa; hakan dan girma da falalar waɗancan dararen da kuma dan neman daren Lailatul Ƙadr.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa akan yawaita alheri da fuskokin ayyukan ɗa'a a cikin watan Ramadan a hade da kuma goman ƙarshe daga gare shi a keɓance.
  • Goman ƙarshe na Ramadan suna farawa ne daga daren ashirin da ɗaya har zuwa ƙarshen wata.
  • An so ribatar lokuta mafifita da ayyukan ɗa'a.