Abu Sa'id Al'khudri yana bada labari cewa Annabi ya kasance yana yin I'itikafin goman tsakiya na Azumi don neman daren lailatul kadari, sai wata shekara yayi -kamar yadda ya saba- har sai da adaren Ashirin da daya, ita ce ranar da yake futowa a safiyarta daga I'itikafinsa, sai ya san cewa lallai daren lailatul kadari tana goman karshe, sai yace da Sahabbansa: Duk wanda yayi I'itikafi tare da ni goman tsakiya, to ya zarce da I'itikafinsa, yayi a goman karshe, kuma ya bada labarin cewa Allah yanuna masa ita a Mafarkinsa sannan ya mantar da shi ita, sai dai ya ce kamar yagani a barcin wasu alamominta a cikin wannan shekarar su ne: Sujadarsa a cikin sallar Asuba akan tabo mai ruwa, to Allah ya gasgata Mafarkin Annabinsa, sai akayi ruwa a daren Ashirin da daya kuma ya kasance Masallacinsa an gina shi ne da yayin danga, kuma kututtudabino shi ne ginshikansa kuma rufinsa na ganyen Dabino ne, to sai Masallacin yayi ta zubar ruwa, sai Annabi yayi Sujada a safiyar Ashirin da daya, a cikin ruwa da tabo, Taisir Allam (349) Tanbih Al'afham (3/472) Ta'asis Al'ahkam 3/292