Annabi Ya kasance yana E'itikafi a cikin kwanaki goman karshe na watan Azumi, cewa Matarsa Safiiya ta ziyarce shi a daya daga cikin dararen sai sukai magana wani lokaci, sannan sai ta tashi domin ta koma gidan ta, sai ya tashi tare da ita don ya rakata, kuma ya dauke mata kewa, sai wasu Mutane biyu daga cikin Mutanen Madina suka wuce, yayin da suka ga Annabi sai sukai sauri a tafiyar su sabida kunyar Annabi yayin da suka ganshi yana tare tare da Iyalinsa, sai ya ce da su ku tafi a hankali cewa ai ita Matata ce Safiyya, sai ce: Tsarki ya tabbata ga Allah kuma shin akwai abunda zai janyo mu munana maka zato, sai ya basu labari cewa: Lallai Shaidan yana matukar Kwadayin batar da Yan Adam, kuma yana da dama mai girma kan haka, domin cewa shi yana gudu ne a jiki kamar yadda jini yake yi, sabida buyan hanyar shigar tasa, da kuma hanyoyin nasa, kuma yaji tsoron kada ya jefa wani abu-Mara kyau- a zuciyar su