explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari game da falalar tsayuwar Lailatul kadari wacce take kasancewa a goman ƙarshe na Ramadan, cewa wanda ya yi ƙoƙarin yin sallah a cikinta da addu'a da karatun al-ƙur'ani da zikiri, yana mai imani da ita, da kuma abin da ya zo a falalarta, yana mai kwaɗayin sakamakon Allah - Maɗaukakin sarki - da aikinsa, ba don riya ko jiyarwa ba, to, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar daren lailatul ƙadri da kwaɗaitarwa a kan tsayuwarsa.
  • Ayyuka na gari ba'a karɓarsu sai tare da gaskiyar niyyoyi.
  • Falalar Allah da rahamarsa, cewa wanda ya tsaya (da ibada) a daren Lailatul ƙadri yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa.