Wasu mazaje daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun gani a cikin mafarki cewa daren Lailatul-ƙadr yana kasancewa ne a ƙarshen daren bakwai na Ramadan. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ina ganin mafarke-mafarkenku haƙiƙa sun dace a bakwan ƙarshe na Ramadan, wanda ya kasance yana nufinsa, yana mai kwaɗayi akan nemansa, to sai ya yi ƙoƙari a kardadonsa da nemansa da yawaitawa daga aiki na gari shi ya fi ƙaunar ya zama a bakwan ƙarshe, shi yana farawa ne daga daren ashirin da huɗu idan watan Ramadan ya zama kwana talatin ne, kuma daren ashirin da uku yana farawa ne idan watan ya zama mai kwana ashirin da tara ne.