Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a kowane yinin da rana zata ɓullo a cikinsa akwai wasu mala'ilku biyu zasu sauka suna masu kira, ɗayansu yana cewa: Ya Allah Ka baiwa mai ciyarwa a ayyukan ɗa'a da iyalai da baƙi da abubuwan alheri mayewa Ka canja masa mafi alheri a cikin abinda ya ciyar, kuma Ka yi masa albarka. Ɗayan kuma yana cewa: Ya Allah Ka bawa mai riƙewa (mai rowa) ɓaci ka halakar da dukiyarsa wacce ya hanata ga waɗanda suka cancanceta.