explain-icon

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bada rabarin cewa idan mutum ya ciyar da iyalinsa waɗanda ciyarwarsu ta wajaba a kansa, kamar matarsa da iyayensa da ‘ya’yansa da sauransu, yana mai neman kusanci zuwaga Allah da hakan, yana neman ladan ciyarwar a wurin Allah, to, Allah zai ba shi ladan sadakarsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Samun lada idan aka ciyar da iyali.
  • Mumini [na gaskiya] yana neman yardar Allah a aikinsa da kuma lada da sakamakon da yake wurin Allah.
  • Ya kamata a halarto da niyya mai kyau a kowanne aiki, daga cikin hakan akwai lokacin ciyar da iyali.