Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci sashin nau’ukan ciyarwa, sai ya ce: Dinarin da ka ciyar da shi a yaƙi a tafarkin Allah, da dinarin da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye da bauta, da dinarin da ka yi sadaka ga miskini mabuƙaci, da dinarin da ka ciyar da shi ga iyalanka, sannan ya bada labarin cewa mafi girmansu a lada a wajen Allah shi ne wanda ka ciyar da shi ga iyalanka da wanda ciyar da shi ya lazimceka.