explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari cewa wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da Allah, yana mai gasgatawa da wajabcin azumin da abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi tanadi na gwaggwaɓan ladaddaki da sakamako, yana mai nufin zatin Allah - Maɗauakakin sarki - da shi ba don riya ko jiyarwa ba, za'a gafarta masa zunubansa da suka shuɗe.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • FALALAR TSARKAKE NIYYA DA MUHIMMANCINSA A AZUMIN RAMADAN DA WANINSA NA AYYUKA NA GARI.