Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi: Dukkan aikin Ɗan Adam ana ninka kyakkyawa da kwatankwacinsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, sai azimi; shi nawa ne riya ba ta shiga cikinsa, kuma nine zan yi sakayya da shi, sai in kaɗaita da sanin gwargwadan ladansa da kuma ninka kyawawan (ladansa). Sannan Ya ce: (Azimi garkuwa ne) kuma kariya ne kuma sitira ne kuma katanga ne mai katangewa daga wuta; domin cewa shi kamewa ne daga sha'awowi da afkawa cikin zunubai, wuta kuma abar kewayewa ce da sha'awowi. (Idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa) da yin jima'i da abubuwan gabatarwarsa, ko mummunan zance kai tsaye. (Kada ya yi zancen banza) da yin husuma da kuma kururuwa. (Idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi) a cikin Ramadan to ya ce: Lallai ni mai azimi ne; wataƙila ya ƙyale shi, idan ya nace sai dai faɗa to a haƙiƙa to sai ya tunkuɗe shi da mafi sauƙi, sai mafi sauƙi kamar wanda ya shigo maka gida. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rantsuwa da wanda ransa yake a hannunSa cewa canzawar bashin bakin mai azimi saboda azimin ya fi daɗi a wurin Allah ranar alƙiyama daga ƙanshin almiski a wurinku, kuma ya fi yawan lada daga almiski abin so gare shi a ranakun juma'a da kuma majalisan zikiri. Mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki da gushewar yunwarsa da kuma ƙishirwarsa saboda yadda aka halatta masa buda baki. Kuma zai yi farin ciki da cikar aziminsa da kuma kammala bautarsa, da kuma sauƙi daga Ubangijinsa, da taimako akan aziminsa na gaba. (Idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa) da sakamakonsa da kuma ladansa.