Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Idan aka ajiye jana'iza (gawa) maza suka ɗauketa akan kafadinsu idan ta kasance ta gari ce zata ce: Ku kaini, idan ba ta gari ba ce kuwa zata ce: Ya kaicanta ina zasu tafi da ita? kowane abu yana jin sautinta sai mutum kawai, da ace ya ji shi (sautin) da ya suma». Ingantacce ne - Bukhari ne ya rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa idan aka ajiye jana'aiza (gawa) akan gado (makara), maza suka ɗauketa akan wuyansu, idan ta kasance ta gari ce zata ce: Ku gabato da ni dan abinda ta gan shi a gabanta na ni'ima, idan ba tagari ba ce zata yi ƙara da sauti abin ƙi: Ya halakarta ina zasu tafi da ita?! dan abinta ta gan shi a gabanta na azaba, kowane abu yana jin sautinta sai mutum kawai, da a ce ya ji shi da ya suma saboda tsananin abinda ya jishi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Mamaci na gari yana ganin abubuwan bushara kafin rufe shi, kafiri kuwa yana kasa haƙuri, kuma yana ganin akasin hakan.
  • Wasu sautukan wanda ba mutum ba zai ji su, amma mutum ba zai iya jinsu ba.
  • Sunna ita ce ɗaukar jana'iza (gawa) akan kafadun maza banda mata; saboda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana mata binta (jana'iza).