Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga masallaci zai ce: (Ina neman tsarin Allah Mai girma) Ina neman tsari ina fakewa ga Allah da kuma siffofinSa (Da fuskarSa mai kyauta) Mai kyauta Mai bayarwa, (Da sarautarSa) RinjayenSa da ikonSa da rinjayenSa akan wanda ya yi nufi daga halittarSa (Madawwami) na tun fi azal na har abada (Daga Shaiɗan abin jefewa) Abin nisantarwa abin korewa daga rahamar Allah, Wato; Ya Allah Ka kiyayeni daga wasiwasinsa da halakarwarsa da tsarinsa da haɗarinsa da ƙawacensa da ɓatarwarsa, domin shi ne sababi a ɓatarwa mai sa halakarwa da jahilci, Aka cewa Abdullahi ɗan Amr "Shin shike nan?" Wato: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi wannan kadai? Ya ce: Eh. Idan mai shiga masallaci ya faɗi wannan addu'ar; Shaiɗan zai ce : Haƙiƙa an kiyaye ran wannan mai shigowar daga gareni dukkanin lokaci, yininsa da darensa.