Dan Mas'ud-Allah ya yarda dashi-yana bamu labari cewa wani Mutum daga Malaman Yahudawa yazo wajan Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-ya ambata masa cewa sun samu cikin Littattafansu cewa Allah -tsarkakekken Sarki-Ranar Al-kiyama zai sanya Sammai a Yatsa,kuma kassai a Yatsa,kuma Bishiyu a Yatsa,kuma Kasa aYatsa,.Awata Riwayar:kuma Ruwa akan Yatsa,kuma sauran ababan Halitta akan Yatsa,dagaYatsunsa-Mai-Girma da Daukaka-,kuma ita Biyarce kamar yadda yazo acikin Riwayoyi ingantattu,kuma ba kamar Yatsun ababan Halitta bace,kuma cewa shi zai bayyana wani abu daga Ikonsa da Girmansa Mai-Girma da Daukaka sannan sai ya girgizasu kuma ya bayyana Mulkinsa na Hakika,da cikar tasarrufinsa saki ba kaidi da Uluhiyyarsa ta Gaskiya.Sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Dariya har Fikokinsa suka bayyana saboda gasgata fadin Malamin Yahudawan,sannan ya karanta:{Kuma basu kaddara Allah akan Hakikanin ikon yinsa ba Kasa duka damkarsa ce a Ranar Kiyama}.