An zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wasu ribatattu daga (ƙabilar) Hawazin, sai ga shi a cikinsu akwai wata mace tana neman ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaron da ta ɗauke shi sai ta shayar da shi saboda cutuwa da tayi ta hanyar taruwar nono a cikin hantsarta, sai ta samu ɗanta a cikin ribatattu sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa sahabbansa: Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta? Muka ce: Ba zata jefa shi da yardarta ba har abada. Sai ya ce: Allah Ya fi jin tausayin bayinSa daga wannan matar da ɗanta.