Musulmn da ya Lazamci zuwa Masallatai don yin Sallah da yin Zikiri a cikin su kuma ya dawwama kan hakan, to Allah Madakaki yana farin ciki da shi, kamar yadda Iyalan Matfiyi suke yi idan ya dawo, kuma bai halatta a fassara kalmar Murna ba da Rahama ko Tausayi ko waninsu, aa ya wajaba a tabbatar da su Sifar Allah Madaukaki ce ba tare da Juyawa ba ko canzawa ko korewa kuma ba tare da kwatantawa ba ko Kamantawa, wannan kuma tare da Sanin cewa Murna tana hade da Tausayi da jin kai, Allah shi ne Mafi Sani.