Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin Allah maɗaukaki Yana sakkowa a kowanne dare zuwa sama makusanciya lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura, yana kwaɗaitar da bayinSa a kan su roƙe shi, shi kuma zai amsawa wanda ya roƙe Shi, yana zaburar da su a kan su tambaye Shi abin da suke so, Shi kuma zai ba wanda ya tambaye Shi, yana kiransu da su roƙi gafararSa daga zunubansu Shi kuma yana gafartawa bayinSa muminai.