explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani kuma ya tsoratar akan wasu ayyukan mutanen Jahiliyya, sai ya ce: Ba ya tare da mu: Na farko: Wanda ya mari kundukuki (kumatu) an keɓanci kundukuki dan kasancewarsa shi ne galibi a hakan, inba haka ba marin sauran fuska yana shiga cikin hanin. Na biyu: Yaga abnida ake buɗewa daga tufa dan kai ya shiga cikinsa saboda tsananin baƙin ciki. Na uku: Yin kururuwa irin ta mutanen Jahiliyya kamar ihu da kaico da halaka da kukan mutuwa da wanin hakan.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Wannan narkon a cikin hadisin yana nuni akan cewa waɗannan ayyukan suna daga cikin manyan zunubai.
  • Wajabcin haƙuri akan masifa, da haramta fushi akan ƙaddarorin Allah masu raɗaɗi, da bayyanar da hakan: Da kukan mutuwa ko aske kai ko yaga riga ko wanin hakan.
  • Haramcin kwaikwayon Jahiliyya da al'amuransu waɗanda mai shari'antawa bai tabbatar da su ba.
  • Babu laifi akan damuwa da hawaye, shi ba ya kore haƙuri akan hukuncin Allah - Maɗaukakin sarki -, kawai shi tausayi ne Allah Ya sanya shi a cikin zukatan makusanta da masoya.
  • Yarda da hukuncin Allah ya wajaba akan musulmi, idan bai yarda ba to haƙuri wajibi ne a kansa.