Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da Annabi - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - a ranar babbar sallah wayewar garin jifan babban Shaidan a hajjin bankwana, sai ya umarce shi ya tsinto masa tsakwankwanin jifa, sai ya tsinto masa tsakwankwani bakwai, kowacce daya daga cikinsu ta kai girman wake ko bunduq, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya sanya su a hannu sa, sannan ya motsa su, ya ce: Ku yi jifa da kwatankwacin wannan a girma, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar daga wuce gona da iri da tsanantawa da ketare iyaka a al'amuran addini, kadai ketare iyaka da wuce gona da iri da tsanantawa a addini shi ya halaka al'ammomin da suka gabata.