explain-icon

Explanation

Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna koyo daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ayoyi goma daga Alkur’ani, ba sa cirata zuwa wasu har sai sun san abinda ke cikin wadannan goman na ilimi kuma suna aiki da shi, sai suka koyi ilimi da aiki gaba daya.

explain-icon

Benefits from the Hadith

  • Falalar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da kwadayinsu akan koyon Alkur’ani .
  • Koyon Alkur’ani yana kasancewa ne da ilimi da aiki da abinda ke cikinsa, ba kawai da karanta shi da kuma hardace shi ba kawai.
  • Ilimi yana kasancewa ne kafin fada da aikatawa .