Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari dan girmamawa a cikin aljanna abinda wani ido bai taɓa ganin zatinsa ba, kuma wani kunne bai taɓa jin siffarsa ba, kuma haƙiƙaninsa bai taɓa afkuwa ko wucewa akan zuciyar wani ɗan Adam ba. Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Idan kun so ku karanta: {Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki (da shi)} [al-Sajda: 17].