Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake yawaita tsinuwa akan wanda bai cancanteta ba to shi ya cancanci uƙuba biyu: Ta farko: Ba zai zama mai shaida ba a ranar alƙiyama akan al'ummu na isarwar Manzanninsu ga saƙonni zuwa garesu, kuma ba za'a karɓi shaidarsa ba a duniya; dan fasiƙancinsa, kuma ba za'a azurta shi da shahada ba ita ce mutuwa a tafarkin Allah. Ta biyu: Ba zai yi ceto ba a ranar alƙiyama lokacin da muminai suke yin ceto ga 'yan uwansu waɗanda suka cancanci (shiga) wuta.