Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana halin tafiya a wani yaƙi a tare da shi akwai sahabbansa Muhajirun da kuma Ansarawa - Allah Ya yarda da su -, sai wani mutum daga Muhajirun ya daki bayan wani mutum daga Muhajirun da hannunsa. Sai mutumin Madinan ya ce: Ku taimakeni yaku Ansarawa, wanda kuma ya yi hijira ya ce: Ku taimakeni yaku Muhajirun, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji sai ya ce: Mene ne wannan? Sai suka ce: Wani mutum ne daga Muhajirai ya daki bayan wani mutum cikin Ansarawa da hannunsa, sai mutumin Madinan ya ce: Ku kawo mini agaji yaku Ansar, wanda ya yi hijira kuma ya ce: Ku kawo min agaji yaku Muhajirun. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ku bar wannan al'adar ta Jahiliyya domin ita mummuna ce abar ƙyama mai cutarwa; ita ce cewa mutum idan abokin rigimarsa ya rinjaye shi sai ya kira mutanensa sai su yi gaggawar taimakonsa alhali shi ne ya kasance azzalimin ko kuma shi ne wanda aka zalinta dan jahilci dake garesu da kuma ƙabilanci. Jabir ya ce: Ansarawa sun kasance lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina yana mai hijira sune mafi yawa, sannan bayan nan Muhajirun suka yi yawa. Sai shugaban munafukai Abdullahi Ibnu Ubayy ibnu Salul ya ce: Al'amarin yakai wannan haddin?! Wallahi idan muka koma Madina sai masu rinjaye - wato yana nufin shi da waɗanda ke tare da shi - sun fitar da ƙasƙantattu - wato yana nufin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da waɗanda ke tare da shi daga Madina. Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah ƙyaleni in daki wuyan wannan munafukin, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ƙyale shi, dan kada mutane su dinga cewa Muhammad yana kashe mabiyansa ko da azahiri ne.