Daga Imran ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum (Aminci ya tabbata agare ku), sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Goma» Sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Ashirin», sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Talatin». Hasan ne - Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Tirmizi da Ahmad da kuma Darimi
explain-icon

Bayani

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum, (Aminci ya tabbata agare ku) sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: An rubuta masa lada goma, sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah, (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada ashirin, sannan wani ya zo sai ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada talatin; wato kowane lafazi yana da lada goma.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Mai zuw shi zai fara wa waɗanda ke zaune sallama.
  • Karin lada (yana kasancewa ne) da ƙarin lafazan sallama.
  • Mafi cika a yin sallama: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma mafificiyar siga a amsa (sallama): Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Kuma aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa).
  • Matakan sallama da amsawa masu wuce juna ne ladan ma haka.
  • Koyawa mutane alheri da kuma faɗakar da su akan samun abinda ya fi.
  • Ibnu Hajar ya ce: Da ace mai fara (sallama) zai ƙara (da rahamar Allah) an so a ƙara (da albarkarSa), da ace zai ƙara (da albarkarSa) shin a shara'anta ƙari a cikin amsawar? haka nan da ace mai fara (sallama) ya yi ƙari akan (da albarkarSa) shin an shara'anta masa hakan, (Imam) Malik ya fitar a cikin Muwaɗɗa daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Sallama tana ƙarewa ne zuwa albarka.