Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da wasu nau’uka uku na mutane, waɗanda suka cancanci uƙubar Allah a ranar alƙiyama da uƙuba uku idan basu tuba ba, ko a gafarta musu uƙubar ba: Ta farko: Allah ba zai yi musu magana ba a ranar alƙiyama saboda tsananin fushinSa, kai zai bijire musu, ko Ya yi musu maganar da ba zata faranta musu rai ba kuma yana nuni akan fushinSa akansu. Ta biyu: Ba zai tsarkakesu ba kuma ba zai yabesu ba kuma ba zai tsarkakesu daga zunubai ba. Ta uku: Azaba mai sa ciwo mai tsanani a lahira ta tabbata agare su. Waɗannan sinfofin na mutane sune: Sinfi na farko: Babban mutum kuma yake afkawa a cikin alfashar zina. Na biyu: Talaka mara dukiya, amma tare da haka yake yi wa mutane girman kai. Na uku: Wanda yake yawan rantsuwa da Allah a cikin saye da siyarwa, sai ya wulaƙanta sunan Allah, kuma ya sanya shi tsani dan samun dukiya.