Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana manyan zunubai cewa su ne waɗanda aka yi narko (alƙawarin azaba) a kan wanda ya aikata su da narko mai tsanani a duniya ko a lahira. Na farkonsu "Yi wa Allah shirka": Shi ne karkatar da kowanne nau'i daga Nau’ukan ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah cikin abin da ya keɓanci Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa. Na biyunsu: "Saɓawa iyaye": Shi ne dukkanin abin da yake nuna cutarwa ga iyaye; magana ce ko aiki, da barin kyautata musu. Na ukunsu "Kashe rai": ba tare da wani haƙƙi ba, kamar kisa a kan zalunci da ta'addanci. Na huɗunsu "Rantsuwa mai dulmiyarwa": Ita ce rantsuwa alhali yana mai ƙarya yana sane cewa ƙarya yake, an ambaceta da hakan; domin cewa tana dulmiya mai yinta a laifi sannan a wuta.