Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi gangancin kashe kansa gargaɗi a duniya cewa za’a yi masa uƙuba a ranar alƙiyama a cikin wutar Jahannama ta irin hanyar da ya yi wa kansa a duniya dan sakamakon da ya dace, wanda ya faɗo daga saman dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wutar Jahannama zai dinga faɗowa a cikinta daga dutsen Jahannama zuwa kwarinta yana madawwami a cikinta, wanda ya kwankwɗi wata guba sai ya kashe kansa da ita to gubarsa tana hannunsa zai dinga kwankwaɗarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya cakawa kansa wani karfe a cikinsa sai ya kashe kansa, to karfensa yana hannunsa zai dinga sukar kansa da shi a cikinsa a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada.