Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa musulmi mai laifi ana yi masa kwadayin afuwar Allah da gafararSa, sai mai bayyanar da sabo dan alfahari da rashin kunya, to ba ya cancantar afuwa; ta inda yake aikata laifi da daddare, sannan ya wayi gari alhali Allah Ya rufa masa asiri, sai ya zantar da waninsa da cewa shi ya aikata sabo kaza jiya, ya kwana Ubangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa!!