Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya buga misali ga nau'i biyu na mutane: Nau'i na farko: Abokin zama da aboki na gari wanda yake shiryarwa ga Allah a abinda a cikinsa akwai yardar Allah, kuma yana taimakawa akan biyayya ga Allah, To kwatankwacinsa kamar mai saida almiski ne, kodai ya baka, ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka samu ka shaƙi ƙanshi mai daɗi daga gare Shi. Nau'i na biyu: Abokin zama kuma mummunan aboki; wanda yake toshe tafarkin Allah, kuma yana taimako akan aikin saɓo, kuma kana ganin mummunan aiki daga gare shi, kuma yana tsawaita maka zargi dan abokantaka da zama da irinsa, to kwatankwacinsa kamar maƙeri ne wanda yake hura wutarsa; kodai ya ƙona maka tufafi daga tartsatsinsa mai tashi, ko ka samu mummunan wari saboda kusantakarsa.