Hakim ɗan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wani abu na jin daɗin duniya sai ya ba shi, sannan ya roke shi karo na biyu sai ya ba shi, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Ya Hakim, lallai cewa wannan dukiyar abar sha'awace abar so ce, wanda ya sameta ba tare da roƙo ba kuma ya karɓeta ba tare da zari da kuma naci ba, za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta da tsinkayar rai da kuma kwaɗayi ba za’a yi masa albarka a cikinta ba, zai zama kamar wanda yake ci ba ya ƙoshi, hannu maɗaukaki mai bayarwa shi ne mafi alheri a wurin Allah daga hannu maƙasƙanci mai roƙo. Hakim ya ce: Sai na ce: Ya Manzon Allah, na rantse da wanda Ya aikoka da gaskiya ba zan karbi dukiyar wani ba ta hanyar roko daga gare shi ba a bayanka har na bar duniya. Halifan Manzon Allah Abubakar - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana kiran Hakim dan ya ba shi rabonsa daga baitul mali, sai ya ƙi karɓar komai daga gare shi, sannan sarkin muminai - Umar - Allah Ya yarda da shi - ya kira shi dan ya ba shi ita, sai ya ƙi karɓarta, sai Umar ya ce: Yaku taron jama'ar musulmai, lallai ni ina ba shi haƙƙinsa wanda Allah Ya raba masa daga ganimar da musulmai suka samu daga kafirai ba tare da ya ƙi ba, sai ya ƙi karɓarta, bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Hakim bai rage dukiyar kowa ba ta hanyar nemanta har ya yi wafati - Allah Ya yarda da shi -.