(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana mamaki daga sha'anin mumini da halayensa ta ɓangaren kyautatawa; hakan domin halayensa dukkansu alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga wani sai ga mumini; Idan farin ciki ya same shi sai ya godewa Allah; sai ya samu lada saboda godiyarsa. Idan kuma cuta ta same shi sai ya yi haƙuri ya nemi lada a wurin Allah, sai ya samu lada saboda haƙuri, shi a kowanne hali yana cikin lada.