Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa bala'i da jarraba ba zasu gushe ba ga bawa mumini da mumina, a kansa da lafiyarsa da jikinsa, da 'ya'yansa na rashin lafiya ko mutuwa ko sabawa ko wanin haka, haka a dukiyarsa na bukatuwa da tafiya kasuwanci da sata, da tawayar rayuwa da kunci a cikin arziki, har Allah Ya kankare masa dukkanin zunubansa da kurarkuransa da wannan bala'in har idan ya gamu da Allah zai zama ya tsarkaka daga dukkan zunubai da kurakuran da ya aikata.