Jarir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da ganin da namiji zai yi wa mace manisanciyarsa bagtatan ba tare da nufi ba? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce shi cewa ya wajaba agare shi ya juyar da fuskarsa zuwa wani ɓangaren da wata nahiyar daban da zarar ya sani, babu laifi akansa.