explain-icon

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labari cewa anbaton Allah (Zikiri) da waɗannan kalmomi masu girma, shi ya fi duniya da abin da yake cikinta, su ne: "Tsarki ya tabbata ga Allah": Tsarke Allah ne daga dukkan tawaya. "Godiya ta tabbata ga Allah": Yabon Allah ne da siffofinSa na Kamala tare da sonSa da kuma girmamaShi. "Babu abin bautawa sai Allah": Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah. Allah ne mafi girma; Mafi girma da ɗaukaka a kan komai.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa a kan anbaton Allah. Kuma Shi ne mafi soyuwa sama da duk wani abu da rana ta fito a kansa.
  • Zaburarwa a kan yawaita anbaton Allah, saboda ladan da yake da shi da kuma falala.
  • Jin daɗin duniya kaɗan ne, kuma sha’awar da ke cikinta mai gushewa ce
explain-icon

kashe kashe

explain-icon

Kari