Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji) kuma abin bautawa da gaskiya mai reno kuma mamallaki shugaba kuma mai gyarawa. (Da Musulunci) da dukkanin hukunce-hukuncensa na umarni da hani (Addini) kuma tafarki da shari'a da miƙa wuya. (Da Annabi Muhammad a matsayin manzo) da Annabi; da dukkanin abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi garemu, sai aljanna ta wajaba gare shi.